Venezuela

Zan iya baiwa sojin Amurka izinin kawar da Maduro - Guaido

Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa, tare da magoya bayansa a birnin Caracas.
Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa, tare da magoya bayansa a birnin Caracas. REUTERS/Andres Martinez Casares

Jagoran ‘yan adawar Venezuela da ya nada kansa a matsayin shugaban kasar na rikon kwarya Juan Guaido, ya ce akwai yiwuwar ya baiwa Amurka izinin amfani da karfin soja wajen tilastawa shugaba Nicolas Maduro sauka daga mulki.

Talla

Guaido ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, zai dauki dukkanin matakai domin ganin ya kawo karshen bala’in karancin abinci da magunguna da kuma matsin tattalin arzikin da al’ummar Venezuela ke ciki.

Sai dai Juan Guaido ya amince cewar, baiwa Amurka damar amfani da karfin soji a Venezuela lamari ne mai cike da sarkakakiya.

Rikicin siyasar Venezuela ya dada rincabewa ne, bayan da shugaban kasar Nicolas Maduro, ya sha alwashin hana shigar da tallafin kayan abinci da magunguna da Amurka ta aikewa ‘yan kasar, kayanda a yanzu haka aka jibge su akan iyakar Venezuela da Colombia.

A halin da ake ciki wata majiya daga fadar White House a Amurka ta ce gwamnatin kasar ta soma tuntubar manyan hafsoshin sojin Venezuela, inda take neman su janye biyayyar da suke wa shugaban kasar Nicolas Maduro.

Wani jami’in gwamnatin Amurka da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a gefe guda, shugaba Trump ya soma shirin kakabawa gwamnatin Maduro karin takunkuman matsi, domin tilasta masa sauka daga mulki.

Majiyar ta ce Amurka na fatan samun karin manyan jami’an sojin Venezuela da za su janye goyon bayansu ga shugaba Maduro, duk da cewa tun bayan kamarin da rikicin siyasar kasar yayi a watan da ya gabata, kadan daga cikin hafsoshin sojin ne suka koma bayan, jagoran ‘yan adawa Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.