Faransa

Mutane sun jikkata a zanga-zangar masu rigunan dorawa

Dubban masu rigunan dorawa a birnin Paris yayinda suka fuskanci 'yan sanda.
Dubban masu rigunan dorawa a birnin Paris yayinda suka fuskanci 'yan sanda. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Zanga-zangar masu sanye da rigunan dorawa da ta gudana jiya Asabar a sassan Faransa, ta juye zuwa tarzoma a birnin Paris, inda aka yi arrangama tsakanin wasu masu zanga-zangar da ‘yan sanda a gaban ginin majalisar dokokin kasar.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce tashin hankali yayi sanadin rasa hannu guda na wani mai zanga-zangar yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kafin kwantarda tarzomar dai, sai da Jami’an ‘yan sandan na Faransa suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake kan gungun masu zanga-zangar da ke kokarin yi mutsu rotse da duwatsu da kuma sauran duk abinda suka raruma.

‘Yan sanda sun ce sun kama mutane 17 daga cikin masu zanga-zangar a Champs-Elysee da kuma harabar majalisar dokokin kasar.

Akalla masu sanye da rigunan dorawar dubu 21 daya ne suka gudanar da zanga-zangar ta jiya a sassan Faransa, ciki har da dubu 4 da suka yi tattaki a birnin Paris kadai domin adawa da shugaba Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.