Turai

Guraben ayyukanyi dubu 600 na cikin hadari a Turai

Jamus za ta fi kowace kasa fuskantar matsalar tattalin arziki, idan Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniya ba.
Jamus za ta fi kowace kasa fuskantar matsalar tattalin arziki, idan Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniya ba. AFP

Wani binciken masana ya ce ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai ba tare da cimma yarjejeniyar rabuwa da ita ba, zai jefa mutane dubu 600 a sasan duniya, cikin hadarin rasa guraben ayyukansu.

Talla

Masanan dake cibiyar bincike ta IWH a Jamus, sun ce rasa guraben ayyukan yin zai tabbata idan kayayyakin da Birtaniya ke saye daga sauran kasashen Turai ya ragu da kashi 25, muddin ta fice daga cikin kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniya ba.

A cewar binciken, ma’aikatan da ke kasashen Jamus da Faransa matsalar za ta fi shafa, ta fuskar rasawa ko dakushewar tasirin ayyukansu, inda masanan suka ce yawan mutanen da lamarin zai shafa a Jamus ya kai dubu dari da uku, sai kuma dubu 50 a Faransa.

Masana tattalin arzikin, sun kara da cewa matsalar za kuma ta iya tilastawa kamfanoni da manyan masana’antun ci gaba da rike ma’aikatan nasu, amma ta hanyar zafatare yanki mai tsoka na albashinsu.

Har yanzu dai babu alamun za’a cimma sabuwar yarjejeniyar rabuwa tsakanin Birtaniya da EU kafin cikar wa’adin 29 ga watan Maris, duka da kokarin Fira Minista Theresa May na shawo kan shugabannin na Kungiyar EU kan yiwa yarjejeniyar Brexit da suka cimma a watan Nuwamban bara kwaskwarima, wadda majalisar Birtaniya ta yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.