Kotun Spain ta fara sauraron shari'ar shugabannin yankin Catalonia
Wallafawa ranar:
Jagororin ‘yan awaren Spain 12, da suka taka rawa wajen kokarin ballewar yankin Catalonia daga kasar, sun gurfana a gaban kotun kolin kasar a yau Talata don fara sauraron shari'ar da ake musu. Fara sauraron shari’ar jagororin ‘yan awaren na zuwa ne dai dai lokacin da rikicin farfado da fafutukar ballewar yankin na Catalonia ke neman dawowa sabo.
Wasu daga cikin ‘yan awaren dai sun shafe sama da shekara daya tsare a hannun jami’an tsaro, kafin bayyanar ta su a gaban kotun kolin ta Spain, inda manyan alkalai 7 ke sauraron shari’ar.
Baki dayan wadanda suka gurfana a yau din na fuskantar shari’a ne kan zaben raba gardamar da suka jagorancin gudanarwa a ranar 1 ga watan Oktoba na 2017, kan neman ballewar Catalonia daga Spain, duk da cewa a waccan lokacin kotun kolin ta haramta shi.
Sai kuma sanawar da suka yi bayan zaben na shelar tabbatar da samun yancin kan Yankin na Catalonia daga Spain, wanda ya wanzu na gajeren lokaci.
Muddin laifukan jagororin ‘yan awaren ya tabbata, za su fuskanci hukuncin daurin shekaru 17 zuwa 25.
Sai dai Carles Puigdemont tsohon shugaban yankin Catalonia da ya tsere zuwa Belgium kwanaki kalilan bayan shelar ballewar yankin daga Spain a ranar 27 ga watan Oktoban 2017, baya cikin manyan jagororin ‘yan awaren da suka gurfana a gaban kotun, dan haka shari’ar ba za ta shafe shi ba, la’akari da cewa ba’a yi wa wanda ake zargi da aikata babban laifi shari’a idan baya nan, a karkashin dokokin kasar Spain.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu