Faransa

Faransa: Za a tanadi hukunci mai tsauri kan kyamar Yahudawa

Wata makabartar Yahudawa da ke birnin Strasbourg, a Faransa.
Wata makabartar Yahudawa da ke birnin Strasbourg, a Faransa. REUTERS/Vincent Kessler

Wani gungun ‘yan majalisar dokokin Faransa, ya gabatar da kudurin doka da ke bayyana kyamar Yahudanci a matsayin babban laifi da zai kai ga dauri a gidan yari.

Talla

Kudurin ya zo a dai dai lokacin da shugaban kasar ta Faransa Emmunel Macron, ke fatan ganin an yanke hukunci mai tsanani a kan wadanda aka samu da wannan laifi.

Sai dai yayin da mahukuntan Faransa ke neman samar da wannan doka, wasu ‘yan kasar kuwa na ganin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan, domin akwai bambanci tsakanin nuna adawa da salon siyasar Isra’ila da kuma nuna kyama ga Yahudanci.

Wannan batu ya dauki hankula ne a fagen Siyasar Faransa, bayan da wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da manufofin shugaba Macron suka nuna wa wani shahararren marubuci da ke kare Yahudanci mai suna Alain Finkielkraut kyama.

Hakan ya sa masu ruwa da tsaki a lamurran siyasar kasar shirya wani taron gangami a ranar Talatar da ta gabata, domin nuna fargaba a game da yadda wannan matsayi ke dada kamari, to sai dai a wannan rana ce wasu mutane suka kai hari akan makarbatar Yahudawa tare da zana alamar ‘yan Nazi a kan kaburbura.

A karkashin dokokin Faransa, nuna kyamar Yahudanci, laifi ne da ake yanke hukunci ga wanda ya aikata shi, tamkar dai laifufuka na nuna wa sauran jama’a wariyar jinsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.