Birtaniya-Turai

Majalisar Birtaniya ta ki yarda da shirin fita daga EU ba yarjejeniya

Zauren Majalisar Birtaniya na mahawara kan Brexit
Zauren Majalisar Birtaniya na mahawara kan Brexit Reuters TV via REUTERS

‘Yan majalisar Birtaniya sun ki amincewa da shirin ficewa daga kungiyar Turai ranar 29 ga wannan wata ba tare da kulla yarjejeniya ba, a wani mataki da ya sake zama koma-baya ga gwamnatin Firaminista Theresa May.

Talla

‘Yan Majalisu 312 suka ki amincewa da shirin, yayin da 308 suka goyi bayansa. Kafin  kada wanann kuri’a Firamista Theresa May ta gargadi ‘Yan Majalisar kan abin da zai biyo baya muddin suka kada kuri’ar watsi da bukatarta.

Bayan kudirin nata ya kasa samun nasara, Firaministar ta bayyana cewa, ‘’Matakin da wannan majalisa ta dauka zai dada raunana dangantakar da ke tsakanin jama’ar Birtaniya da wakilan majalisar’’.

Shugaban Jam’iyyar Labour dake jagorancin ‘Yan adawa Jeremy Corbyn ya ce tun da Firaminista May ta gaza daukar matakan da suka dace a cikin shekaru biyu, su suna da shirin da yafi nata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.