Turai

Mutane gommai suka hallaka a wani harin yan bidinga a New Zealand

Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni a harin Christchurch na kasar New Zealand
Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni a harin Christchurch na kasar New Zealand TVNZ/via REUTERS TV

A Kasar New Zealand mutane gommai sun hallaka, bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan masu ibada a wasu masallatan Juma’a biyu da ke birnin Chrischurch a yau Juma’a, inda suka jikkata wasu 20.

Talla

Yan Sanda a kasar New Zeland da safiyar  yau juma’a a cewar Shugaban ‘yan sandan yankin Mike Bush sun yi nasarar kama mutane 4, kuma tuni suka dauki matakan kariya .

Firaministar kasar ta bayyana cewa ,hukumomin kasar zasu dau matakan da suka dace wajen kare al'uma daga hare-haren yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.