New Zealand

Dan ta'addan da ya hallaka Masallata 49 ya gurfana a gaban kotu

Brenton Tarrant dan bindigar da ya hallaka Masallata 49 a wasu Masallatan Juma'a 2 da ke New Zealand, a tsakiyar jami'an tsaro.
Brenton Tarrant dan bindigar da ya hallaka Masallata 49 a wasu Masallatan Juma'a 2 da ke New Zealand, a tsakiyar jami'an tsaro. Mark Mitchell/New Zealand Herald/Pool/REUTERS.

Jami’an tsaron New Zealand sun gurfanar da dan ta'addan da ya bude wuta kan Masu Ibada a wasu Masallatan Juma’a biyu da ke birnin Christ-church a gaban kotu, bayan da ranar Juma'a ya hallaka Masallata 49 tare da jikkata wasu adadi mai yawa.

Talla

An gurfanar da dan bindigar Brenton Harrison, dan kasar Australia mai shekaru 28 a gaban babbar kotu da ke birnin na Christchurch a yau Asabar, wadda ta bada umarnin a ci gaba da tsare shi, zuwa 5 ga watan Afrilu, lokacin zamanta na biyu a kan ta’addancin da yayi.

Harin ta’addancin na ranar Juma’a dai ya sa Fira Ministar New Zealand Jacinda Ardern shan alwashin sake tsaurara dokokin mallakar bindiga a kasar, tun bayan makamancin matakin da gwamnatin kasar ta taba dauka a shekarar 1992, lokacin da wani dan bindiga ya hallaka mutane 13 ta hanyar bude musu wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.