New Zealand

Firaminista ta sha alwashin hukunci mai tsanani kan dan ta'adda

Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden, yayin ganawa da iyalan Masallatan da dan ta'adda ya hallaka.
Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden, yayin ganawa da iyalan Masallatan da dan ta'adda ya hallaka. New Zealand Prime Minister's Office/Handout via REUTERS.

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta sha alwashin hukunci mai tsanani kan dan bindigar da ya kai hari Masallachin Juma’a, inda ya hallaka mutane 50 a makon jiya.

Talla

Yayin bude zaman Majalisar kasar yau, wadda ta fara da yin Sallama irin na addinin Islama, Assalamu alaikum, Ardern tace babu makawa Dan bindigar zai fuskanci fushin hukuma kamar yadda doka ta tanada.

Firaministar tace saboda kyamar aika aikan da dan bindigar yayi, ta daina kiran sunan sa, saboda shi dan ta’adda ne, mai laifi ne kuma mai tsatsauran ra’ayi.

Yayin kammala jawabin ta a zauren majalisar, Firaminista ta bayyana goyan baya ga al’ummar Musulmin kasar, inda take cewa ‘Wa alaikumus Salaam wa rahmatullah wa barakatuhu’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.