Isa ga babban shafi
Serbia

Karadzic na Serbia zai cigaba da zaman yari tsawon rayuwarsa

Tsohon shugaban Serbia Radovan Karadzic
Tsohon shugaban Serbia Radovan Karadzic Robin van Lonkhuijsen / POOL / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Alkalan Kotun duniya da ke shari’ar laifuffukan yaki yau sun yanke hukuncin cigaba da zama a gidan yari har iya rayuwar tsohon shugaban Sabiya, Radovan Karadzic saboda samun sa da laifuffukan yaki daban daban.

Talla

Alkalan sun amince da hukuncin da aka yankewa Karadzic a shekarar 2016, kana suka kara masa karin shekaru 40 bayan kin amincewa da daukaka karar da ya yi.

Alkali Vagn Joensen ya ce alkalan da suka yankewa Karadzic shari’ar farko, basu fahimci irin girman laifin da ya aikata ba.

Kotun ta samu tsohon shugaban ya jagoranci kashe maza da matasan al’ummar Musulmi da ke Srebenica da kuma fararen hula a Sarajevo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.