Brexit

Majalisar Birtaniya ta sake yin watsi da yarjejeniyar Brexit

Fira Ministar Birtaniya Theresa May a zauren majalisar dokokin kasar.
Fira Ministar Birtaniya Theresa May a zauren majalisar dokokin kasar. PRU / AFP

A karo na uku, ‘yan majalisar Birtaniya sun sake yin watsi da yarjejeniyar Brexit ta rabuwar kasar da kungiyar kasashen Turai EU.

Talla

‘Yan majalisa 344 ne suka yi watsi da yarjejeniyar, yayinda 286 suka kada kuri’ar amincewa da ita.

Matsayar ‘yan majalisun dai na nufin zabin da ya ragewa Birtaniya, shi ne ficewa daga cikin kungiyar EU a ranar 12 ga watan Afrilu, kuma ba tare da cimma yarjejeniya kan yadda alakarsu za ta kasance ba.

Yayi jawabi a zauren majalisar bayan yin watsi da yarjejeniyar, Fira Ministan Birtaniya Theresa May ta bayyana matakin a matsayin babban koma baya, da ka ya jefa kasar cikin wani hali.

Shi kuwa jagoran ‘yan adawa na jam’iyyar Labour Jeremy Corbyn kira yayi ga Fira Ministar ta yi murabus, tare da bukatar gudanar da sabon zabe na kasa domin gaggauta warware matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.