Venezuela

Matsalar rashin lantarki na dada kamari a Venezuela

Daya daga cikin daruruwan masu zanga-zanga a Venezuela kan matsalar rashin wutar lantarki da ruwan sha.
Daya daga cikin daruruwan masu zanga-zanga a Venezuela kan matsalar rashin wutar lantarki da ruwan sha. AFP/Federico PARRA

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya bayyana matakin gwamnatinsa na soma aiwatar da tsarin kasaftawa yankunan kasar hasken lantarki, daya bayan daya, saboda matsalar karancin wutar da ilahirin kasar ke fuskanta sama da makwanni 3.

Talla

Bayyana Wannan matakin dai ya zo ne jim kadan bayan da shugaba Maduro ya bada umarnin rage sa’o’in da ma’aikata ke yi a bakin aiki, da kuma rufe makarantun kasar saboda matsalar karancin hasken lantarkin da ta yi kamari.

Ci gaba da fuskantar matsalar ce ta sanya dubban ‘yan adawa gudanar da zanga-zanga ranar Lahadi a birnin Caracas.

Sau uku Venezuela ta fuskanci matsalar rashin hasken lantarkin a watan Maris da ya gabata, inda kuma yanzu haka, jihohi 20 daga cikin 23 dake kasar ne basu da lantarkin ciki harda babban birnin kasar Caracas.

Kungiyar injiniyoyin kasar ta Venezuela a baya bayan nan sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ma’aikatar samarwa da rarraba hasken lantarkin kasar na iya samar da mega watts dubu 5 zuwa 6 ne kawai na karfin wutar lantarkin, a maimakon megawatts dubu 34 da kasar ta saba samu a baya.

Yayinda shugaban kasar Nicolas Maduro ya zargi Amurka da hannu wajen haddasa matsalar, shi kuwa Jagoran ‘yan adawa mai samun goyon bayan kasashe 50, dake ayyana kansa a matsayin halastacce shugaba, Juan Guaido, ya bukaci ‘yan kasar da su cigaba da zanga-zanga ba kakkauatawa, har sai sun cimma burin kawo karshen shugabancin Maduro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI