Turai

Binciken Panama ya taimaka wajen kwato sama da dala biliyan 1 na haraji

Les enquêteurs allemands ont pour leur part rapatrié Daga watan Agusta na 2016 zuwa yanzu, an gudanar da bincike kan laifukan gujewa biyan haraji har kashi 500.
Les enquêteurs allemands ont pour leur part rapatrié Daga watan Agusta na 2016 zuwa yanzu, an gudanar da bincike kan laifukan gujewa biyan haraji har kashi 500. KACPER PEMPEL/REUTERS

Shekaru uku bayan bankado badakalar Panama Papers", ta kaucewa biyan haraji, kasashe 22 da ke fama da matsalar sun yi nasarar kwato kimanin dalar Amruka bilyan 1 da miliyan 200 da aka karkatar.

Talla

Kasa ta farko daga cikin jerin kasashen da ta kwato adadi mafi yawa na kudaden da aka karkatar don gujewa harajin ita ce, Britaniya wadda ta yi nasarar karbo dala miliyan 252.

Jamus ke biye da ita, wadda ta kwato dala miliyan 183 sai kuma ta ukunsu Faransa da ta karbo adadin dalar Amruka miliyan 136, da aka karkatar.

Jaridar Le Monde ta bayyana cewa, a Faransa inda yanzu haka aka rufe binciken, kasar ta karbi kimanin euro miliyan 120, da suka hada da kudaden tara da kuma na gyaran hali.

Daga watan Agusta na 2016 zuwa yanzu, an gudanar da bincike kan laifukan gujewa biyan haraji har kashi 500, wanda ya bada damar gano badakalar karkatar da kudaden guda 415.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI