EU-Birtaniya

EU ta goyi bayan ganawar May da 'yan adawa kan Brexit

Tutocin Tarayyar Turai da Birtaniya
Tutocin Tarayyar Turai da Birtaniya REUTERS/Tom Jacobs

Babban jami'in Tarayyar Turai EU, mai jagorantar tattaunawa da Birtaniya kan shirinta na ficewa daga cikin kungiyar, Michel Barnier, ya goyi bayan ganawa tsakanin Firaminista Theresa May da ‘yan adawa don warware takaddamar da ta hana ‘yan Majalisar Dokokin Kasar amincewa da yarjejeniyar Brexit.

Talla

Yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa a yau Alhamis tsakanin uwargida May da jagoran babbar jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn dangane da kaucewa fitar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Sau uku ‘yan Majalisar Birtaniya suna yin watsi da yarjejeniyar Brexit da May ta cimma da shugabannin kungiyar kasashen Turai.

Kazalika shugabancin Kungiyar Tarayyar Turan EU na ci gaba da kosawa kan tsaikon da ake fuskanta kan ficewar kasar ta Birtaniya daga cikinta, bayan shafe kimanin shekaru 46 a matsayin mamba a cikinta.

A ranar 12 ga watan Afrilu da muke ciki aka tsara Birtaniya za ta kammala ficewa daga cikin kungiyar EU, sai dai har yanzu babu tabbas kan ko yunkurin Firaministar Birtaniya kashi na 4 zai yi nasarar gamsar da ‘yan majalisun kasar har su amince da yarjejeniyar fita daga cikin gungun kasashen Turan da ta cimma da shugabannin kungiyar ta EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.