Turai

Alkali ya bukaci binciken lafiyar dan ta’addan New Zealand

Brenton Harrison Tarrant, mutumen da ya kashe mutane 50 a New Zeland
Brenton Harrison Tarrant, mutumen da ya kashe mutane 50 a New Zeland REUTERS/Mark Mitchell

Wani Alkali a kasar New Zealand ya bada umurnin gudanar da binciken lafiyar dan ta’addan da ya harbe Musulmi 50 a Masallatan juma’ar dake kasar, Brenton Tarrant, domin tabbatar da ko yana da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a.

Talla

Tarin mutanen da suka tsira daga harin sun taru a cikin kotun, inda wanda ake zargin ya bayyana ta kafar bidiyo daga gidan yarin da ake tsare da shi domin amsa tambayoyi.

Shi dai Terrant na fuskantar tuhumar kisan kai na mutane 50 da kuma yunkurin kisan kan mutane 39 a harin da ya girgiza Duniya.

Alkalin kotun Cameron Mender ya yanke hukuncin cewa masu kula da lafiya biyu zasu duba lafiyar dan ta’addan kafin yiwa kotu bayani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI