Birtaniya-Turai

Birtaniya ta fara bayar da sabon Passport marar tambarin EU

Birtaniya ta fara bayar da Passport ba tare da tambarin Tarayyar Turai a jikinsa ba, duk kuwa da matakin tsawaita lokacin ficewar kasar daga gungun kasashen na Turai, dama takaddamar siyasar da ta kunno ka igame da ficewar.

Firaminista Theresa May
Firaminista Theresa May Jack Taylor / POOL / AFP
Talla

Ministan harkokin cikin gida na Birtaniyar, ya sanar da cewa sun dauki matakin fara bayar da Passport din ba tare da tambarin EU tun daga ranar 30 ga watan Maris, ranar da a hukumance ke nufin sun kammala ficewa daga kungiyar ko da dai ba a cimma yarjejeniya ba.

Theresa May dai ta bukaci shugabancin EU ya kara mata wa’adin ficewa don gujewa kammala fita ba tare da yarjejeniya ba, bayan da Majalisar kasar har sau 3 ta yi watsi da kunshin yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ta EU.

Gabanin taron EU a larabar mako mai kamawa, May ta sake mika bukatar kara mata wa’adin ficewar zuwa 30 ga watan Yunin shekarar nan, wanda ta ce a ranar ne kasar za ta kawo karshen alakar shekaru 46 tsakaninta da kungiyar ta Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI