Masu zanga-zangar riguna dorawa a Faransa sun fita a karo na 21
Dubban masu adawa da Gwamnatin Faransa yau sun sa ke fita zanga zanga a karo na 21, don sake nuna bijirewar su da manufofin shugaba Emmanuel Macron, a daidai lokacin da gwamnati ke shirin gabatar da sakamakon rahotan mahawara ta kasa da shugaba Macron ya jagoran ta a sassan kasar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce cikin wuraren da aka gudanar da zanga zangar sun hada da biranen Rouen da Lyon tare da birnin Paris, inda masu zanga zangar ke dauke da allunan da ke tir da manufofin shugaban kasar.
Bayanai sun ce an samu arangama tsakanin wasu masu zanga zangar da suka rufe fuskokin su da Yan Sanda a garin Rouen, sai dai matsalar ba ta yi kamari ba.
Alkaluman ma’aikatar cikin gida sun ce akalla mutane 6,300 suka shiga zanga zangar, kuma 3,100 sun fito ne a birnin Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu