Faransa

Gwamantin Faransa zata aiwatar da sabon tsarin tattalin arziki a kasar

Édouard Philippe, Firaministan Faransa
Édouard Philippe, Firaministan Faransa Philippe LOPEZ / AFP

Gwamnatin Faransa ta soma duba wasu daga cikin bukatun yan kasar ,bayan da aka share yan kwanuki ana tafka muhara dangane da batutuwan da suka jibanci tattalin arzikin kasar .An jima yan kasar ta Faransa na kallon Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron a matsayin dutsen nika.

Talla

A yau litinin kafafen yada labaren kasar sun share lokaci suna ta nuna yan kasar a lokacin tattaunawa kai tsaye da Shugaban kasar Emmanuel Macron, inda suka nuna masa karara cewa siyasar sa ta fuskar tattalin arziki ba za ta haifar da damin ido ba.

Wasu daga cikin yan kasar sun bayyana ta yada wannan gwamnati ke kokarin talautar da marasa karfi, sun kuma hango cewa masu hannu da shuni na amfana da wannan gajiya da Gwamnati take kokarin kawowa.

Ga baki daya Shugaban kasar Emmanuel Macron ya dau alkawalin sake duba rawar siyasar da gwamnatin sa zata taka nan gaba, da nufin samarwa al’uma kayakin more rayuwa cikin wadata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.