EU-Birtaniya

EU ta karawa Birtaniya wa'adin watanni 6 kan Brexit

Shugabannin Kasashen Turai sun amince su bai wa Birtaniya karin watanni shida domin amincewa da yarjejeniyar ficewa daga kungiyar amma bisa sharudda, bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a Brussels.

Shugaban Majalisar Turai Donald Tusk tare da Firaministar Birtaniya Theresa May a taron Brussels 2019-04-10
Shugaban Majalisar Turai Donald Tusk tare da Firaministar Birtaniya Theresa May a taron Brussels 2019-04-10 Olivier Hoslet/Pool via REUTERS
Talla

Cikin yarjejeniyar da aka kulla kan sake karawa Birtaniyar wa'adin shi ne matukar kasar ta kasance a cikin kungiyar ta Turai zuwa bayan ranar 22 ga watan Mayu, ya zama wajibi ga 'yan kasar su shiga zaben Majalisar Turai da za’ayi, ko kuma su fice ranar 1 ga watan Yuni.

Shugaban kungiyar ta EU Donald Tusk, ya ce Majalisar Turai ta amince ta bai wa Birtaniya damar Karin lokaci ne har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba bisa amfani da tanadin doka ta 50 a kundin tsare-tsaren kungiyar.

A cewar Donald Tusk a tsawon watanni 6 da Birtaniya ta samu kari daga EU damar daukar mataki ya rataya a wuyanta, ko dai ta amince da yarjejeniyar da aka cimma ko kuma ta dakatar da karin lokacin.

Tuni Firaministar Birtaniya Theresa May ta bayyana cewa kasar za ta yi iyakar kokarinta wajen ganin ba ta haura 22 ga watan Mayu a cikin kungiyar ta EU ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI