Brexit-EU

Theresa May na neman goyon bayan bangaren adawa kan Brexit

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May ©UK Parliament/Mark Duffy/Handout via REUTERS

Wani babban jami’in gwamnatin Birtaniya, ya ce Theresa May za ta ci gaba da tattaunawa da Jam’iyyar adawa ta Labour cikin mako mai kamawa don ganin ta samu goyon bayan bangaren adawar game da shirin kasar na ficewa daga Tarayyar Turai da ma amincewa da yarjejeniyar da ta kulla da shugabannin EU.

Talla

David Lidington wanda ke matsayin mataimaki na musamman ga Theresa May, ya ce su na amfani da damar da ke hannunsu don ganin sun samu gamsasshen bayanin da Firaministar za ta gabatar gaban zaman majalisa bayan dawowa daga hutun Easter a ranar 23 ga watan nan.

A cewarsa yanzu haka May na zayyana bangaren adawar, abin da yarjejeniyar ta kunsa game da makomar ma’aikata, tsaro da kuma muhalli bayan kammala ficewar kasar daga EU.

Theresa May dai na fatan kammala ficewa daga kungiyar ta EU kafin ranar 23 ga watan Mayu don kaucewa shiga zaben kungiyar da zai gudana a ranar.

A makon da ya gabata ne dai Firaministar ta bukaci karin wa'adi zuwa 30 ga watan Yuni a karo na biyu, game da shirin ficewar kasar daga EU, wanda kuma kungiyar ta gindaya mata sharadi kan ko dai ta fice kafin watan na Yuni ko kuma ta zauna zuwa nan da watanni 6 masu zuwa tare da shiga zaben kungiyar na watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.