Faransa-Macron

Macron ya sha alwashin sake gina Notre-Dame

Shugaba Emmanuel Macron, yayin jawabansa bayan nasarar kashe gobarar Notre-Dame
Shugaba Emmanuel Macron, yayin jawabansa bayan nasarar kashe gobarar Notre-Dame REUTERS/Philippe Wojazer/Pool

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha alwashin sake gina Majami’ar Notre-Dame cikin shekaru 5 masu zuwa, dai dai lokacin da ilahirin majami’un Faransar ke shirin kada kararrawarsu a yau Laraba sa’in da za a cika sa’o’i 48 da gobarar.

Talla

A cewar shugaba Emmanuel Macron ya zama wajibi a garesu su sake gina majami'ar la'akari da muhimmanci da kuma dogon tarihinta a duniya.

Da misalin karfe 3 na daren Litinin ne dai jami’an kwana-kwana suka yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Majami’ar ta Notre Dame da ke birnin Paris daya daga cikin wuraren ibaba mafi dadewa a duniya.

Mujami’ar wadda aka gina kusan shekaru 900 da suka gabata, ta kasance wuri mafi daukar hankalin maziyarta a yankin Turai baki daya, in da ake samun baki kimanin miliyan 13 da ke ziyartar Cocin a kowaacce shekara.

Yanzu haka dai Attajirai da gwamnatoci sun alkawarta bayar da tallafin Euro miliyan 700 don sake gina Majami’ar ta Notre- Dame.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Macron ya ce, "wannan mujami’a, za mu sake gina ta, domin kuwa cibiya ce da ke alamta kasar Faransa, tun daga wannan Talata, zan bayar da umurnin fara wannan aiki"

"Idan ta kama za mu nemi kwararru hatta daga kasashen ketare domin sake gina wannan mujami’a." in ji Macron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.