Amurka-EU-Canada

EU da Canada za su kalubalanci Amurka kan kamfanoninsu a Cuba

Babbar Jamai'ar Diflomasiyyar Tarayyar Turai Federica Mogherini
Babbar Jamai'ar Diflomasiyyar Tarayyar Turai Federica Mogherini . REUTERS/Francois Lenoir

Kungiyar Tarayyar Turai da Canada sun sha alwashin mayar da martani kan Amurka, dangane da matakin da ta dauka na shirin gurfanar da kamfanonin kasashensu a gaban kotun kasar ta saboda harkokin da suke yi a kasar Cuba.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da cewar, daga ranar 2 ga watan Mayu mai zuwa, Amurka za ta janye dokar da ta bai wa wadannan kamfanonin kasashen duniya damar cigaba da hada hada a Cuba, wanda zai bata damar gurfanar da su a kotun ta don hukunta su.

Sanarwar hadin gwuiwa da kungiyar Turai da Canada suka bayar kan matakin, mai dauke da sanya hannun shugabar diflomasiyar kungiyar Federica Mogherini da kwamishiniyar kasuwancin Turai, Cecilia Malmstrom da minister harkokin wajen Canada Chrystia Freeland ta bayyana cewar, matakin na Amurka ya sabawa dokokin duniya.

Sanarwar ta ce a shirye suke su yi aiki tare don kare kamfanonin kasashensu da muradun su a Cuba, yayin da Sakataren harkokin waje Mike Pompeo ya ce ba za su ragawa duk wani kamfani ko kuma wata kasa ba.

Kasashen Spain da Faransa da Jamus da Canada ke da akasarin kamfanonin da ke hada hada a kasar ta Cuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI