Anne Hidalgo ta jagoranci bikin yabo ga jami'an kwana-kwana a Paris
Mazauna birnin Paris, musamman zababbu magadan gari da ‘yan majalisun birnin, sun gudanar da bikin karrama jami’an kwana-kwana, da sauran wadanda suka taka rawa wajen ceto Mujami’ar Notre- Dame na birnin Paris, da gobara ta lakume ginin mai tarihi.
Wallafawa ranar:
An gudanar da wannan gaggarumin biki a dandalin ma’aikatar magajin garin birnin Paris, jim kadan bayan da shugaban kasar Emmanuel Macron ya karrama su tare da basu lambar yabo a fadar gwamnatin kasar ta Elysee.
Anne Hidalgo itace magajiyar birnin na Paris ta jin-jinawa daukacin mutanen da suka taka gaggarumar rawa wajen kashe gobara da ta lakume ginin Notre Dame dake Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu