Ireland

An kashe 'yar jarida a tarzomar Ireland

Lyra McKee, 'yar jaridar da aka kashe a tarzomar Arewacin Ireland
Lyra McKee, 'yar jaridar da aka kashe a tarzomar Arewacin Ireland Facebook

Kungiyar Kasashen Turai ta yi tir da tashin hankalin da ya barke a Arewacin Ireland wanda ya kai ga kashe wata ‘yar jarida, abinda da jami’an ‘yan sanda ke kallo a matsayin ta’addanci.

Talla

Mai magana da yawun Hukumar Kungiyar Kasashen Turai, ya ce, sun bibiyi rahotannin da aka watsa ta kafafen yada labarai game da wannan tashin hankalin na Arewacin Ireland, abinda ya ce, sun yi tir da shi tare da fatan cewa, mahukuntan Birtaniya za su gudanar da bincike kan rikicin da ya yi sanadin kisan ‘yar jaridar mai suna Lyra McKee.

Rahotanni na cewa, wani mutun ne daga cikin masu adawa da manufofin gwamnati ya yi harbi kan gidajen jama’a a Creggan da ke birnin Londonderry, harbin da ya raunata ‘yan jaridar kafin daga bisani ta sheka lahira.

Gabanin kisan nata, McKee ta wallafa wani hoto a shafin sada zumuta, in da ta bayyana halin da yankin ke ciki.

Har ila yau, hotunan da aka watsa ta kafafan sada zumunta sun nuna motoci na ci da wuta, sannan ga jama’a na cilla wutar acibalbal ga jami’an ‘yan sanda.

Tuni jami’an ‘yan sandan suka ce, suna kallon kisan ‘yar jaridar mai shekaru 29 a matsayin ta’addanci kuma suna gudanar da bincike akai.

Marigariyar ‘yar jaridar ta yi aiki da Mujallar Atlantic da kuma Buzzfeed News, yayinda Mujallar Fobes ta sanya ta cikin mutane 30 ‘yan kasa da shekaru 30 da suka yi fice a harkar jarida a shekarar 2016.

Wannan rikicin dai, ya tunatar da tashin hankalin da ya barke a Arewacin Ireland shekaru da dama da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI