Rasha na fatan karfafa huldar kasuwanci da Faransa
Wallafawa ranar:
Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ke ganawa da tawagar manyan ‘yan kasuwar Faransa a fadar sa ta Kremlin cewa Rasha na a cikin shiri domin cigaba da harkokin kasuwanci da kasar Faransa.
A cikin watan fabrairun da ya gabata ne Amurka ta cafke wani hamshakin dan kasuwar Rasha mai suna Michael Calvey da wasu aminansa na kasuwanci da suka hada da wani bafaranshe mai suna Philuppe Delpal, lamarin da ya haifar da fargaba ga wasu ‘yan kasuwa da ke alaka da Rasha.
Faransa na daga cikin kasashen dake adawa da matakin shiga tattaunawa da Amurka bangaren kasuwanci da makamancin haka.
Gwamnatain Faransa da jimawa ta tsaya kai da fata don kare murradun ta bangaren kasuwanci da manyan kasashen Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu