Faransa-Zanga-Zanga

'Yansanda sun kame masu zanga-zanga fiye da 100 a Faransa

dandazon masu zanga-zanga lokacin da su ke kone-kone a birnin Paris
dandazon masu zanga-zanga lokacin da su ke kone-kone a birnin Paris REUTERS/Gonzalo Fuentes

Rundunar ‘yan sandan Faransa, ta ce ta kama fiye da mutane 100 cikin masu zanga-zanga sanye da yaluwar riga, bayan arangama tsakaninsu, dai dai lokacin da su ke gangamin mako-mako karo na 23.

Talla

Rahotanni sun ce an dau sa’o’i kalilan ana zanga-zangar cikin lumana bisa sa idon jami’an ‘yan sandan kafin daga bisani rikici ya barke tsakaninsu wadda ta kai ga amfani da barkonon tsohuwa don kame masu tayar da rikicin.

Rundunar ‘yan sandan ta ce yanzu haka ta kame mutane 126 wadanda suka rika jifan ‘yan sandan tare da kona ababen hawa baya ga ture shingayen binciken ‘yan sanda a birnin Paris.

Akalla 'yan sanda dubu 11 ne suka sanya idanu kan masu zanga-zangar wanda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce yawansu a wannan mako ya kai dubu 9 da 600 kasa da na makon jiya.

Sai dai masu shirya zanga-zangar sun ce adadin da suka fito zanga-zanagr ya ninka adadin da ma'aikatar ke sanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI