Turai

Faransa ta kaddamar da binciken sayar da makamai zuwa Yemen

Yakin Yemen inda aka gano cewa Faransa ta sayar da makamai
Yakin Yemen inda aka gano cewa Faransa ta sayar da makamai Saleh Al-OBEIDI / AFP

Gwamnatin Kasar Faransa ta kaddamar da bincike kan yadda wasu takardun bayanan asiri na sojin kasar da ya shafi amfani da makaman kasar a Yemen da Saudi Arabia da Daular Larabawa suka bayyana a idan jama’a

Talla

Kafofin yada labaran Faransa ne suka wallafa wadannan bayanai dake cikin shafuka 15 da suka kunshi makamai da tankunan yakin da jiragen sama da jiragen ruwan dake daukar tankuna da Faransa ta baiwa kasashen biyu a watan Oktobar bara.

Gwamnatin tace bayyana bayyanan asirin sojin babbar barazana ce ga asirin kasa.

Faransa wadda itace ta 3 wajen sayar da makamai a duniya, na kallon Saudi Arabiya da Daular Larabawa a matsayin manyan abokan cinikin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI