Faransa-Zanga-Zanga

Masu zanga-zangar yaluwar riga sun yi watsi da sabon tsarin Macron

Jagororin masu zanga-zanga sanye da yaluwar riga a Faransa sun yi watsi da sabon matakin shuagaba Emmanuel Macron na zabtare harajin da zai amfani magidanta miliyan 15 galibi masu karamin karfi a kasar.

Wasu masu zanga-zanga a Faransa
Wasu masu zanga-zanga a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

A cewar Thierry-Paul Valette, jagora kuma wanda ya assasa zanga-zangar ta masu yaluwar riga a sassan kasar ta Faransa, za su ci gaba da borensu kamar yadda suka saba kowanne mako, don kuwa a cewarsa shugaban kasar Emmanuel Macron ya rasa gwaggwabar damar shawo kansu tsawon watanni 6.

Tun tsakiyar watan Nuwamban bara aka fara zanga-zangar kan matsin rayuwa a Faransar, inda masu zanga-zangar ke zargin shugaba Emmanuel Macron da kawo sabon tsarin talauta talakawa tare da arzurta masu hali.

Sai dai a baya-bayan nan ana samun raguwar masu fitowa zanga-zangar tun bayan da shugaban ya dauki matakin fara wata mahawarar kasa baki daya da ta bude kofa ga duk mai korafi ga gwamnatinsa, ko da dai jagorin sun ce babu wata raguwa da ake samu a yawan masu fitowar.

A yau Asabar ne dai masu zanga-zangar za su fito gangami karo na 24, inda a kowanne mako ake fuskantar arangama tsakaninsu da jami'an 'yan sanda har ta kai ga kame da dama daga cikinsu.

Tuni dai wasu Faransawa galibi masu karamin karfi su ka yi maraba da sabon matakin na Macron da ya sanar a jiya Juma’a wanda zai samar da saukin rayuwa, wato don magance kalubalen da gwamnatin Macron ta fuskanta da ya harzuka ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI