Venezuela

Sojin Venezuela za su kare kasarsu daga mamayar Amurka - Maduro

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro tare da dubban dakarun rundunar sojin kasar a birnin Caracas.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro tare da dubban dakarun rundunar sojin kasar a birnin Caracas. Miraflores Palace/Handout via REUTERS

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya umarci dakarun kasar da su kasance cikin shiri, domin akwai yiwuwar Amurka za ta iya afka musu da yaki a kowane lokaci.

Talla

Maduro ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wata cibiyar sojin Venezuela da ke arewa maso yammacin kasar, bayan jagorantar wani tattaki tare da manyan hafsoshin sojinsa, tare da wasu dakaru akalla dubu 5.

Matakin na shugaba Maduro ya zo dai dai lokacin da a ranar Asabar, shi ma jagoran ‘yan adawa Juan Guaido ya jagoranci nasa tattakin a zuwa wasu sansanonin sojin Venezuela domin neman goyon bayansu kan aniyarsa ta kawo karshen mulkin Maduro.

A Larabar da ta gabata, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa akwai yiwuwar daukar matakin soji kan gwamnatin Nicolas Maduro, domin kawo karshen rikicin siyasar Venezuela da ya ki ci, yaki cinyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI