Faransa ta tabbatar da sayar wa Saudiya makaman yaki a Yemen
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Faransa ta tabbatar da shirinta na dakon sabbin makamai zuwa Saudiya a daidai lokacin da ake zargin mahukuntan birnin Riyadh da amfani da wadannan makamai wajen murkushe al’ummar kasar Yemen mai fama da rikici.
Ministar Tsaron Faransa, Florence Parly ta shaida wa gidan talabijin na BFM cewa, nan ba da jimawa ba, za a loda makaman a manyan sundukan jiragen ruwa don shigar da su Saudiya a wannan Laraba.
Kodayake Minisatar ta ki fayyane na’ukan makamai, yayinda ta jaddada cewa, Saudiya na amfani da su ne wajen kare kanta tun bayan da ta fara kai hare-hare a Yemen a shekarar 2015.
Ministar ta kuma bayyana cewa, babu wata hujja da ke nuna cewa, al’ummar Yemen sun tagayyara ne sakamakon yadda Saudiyan ke amfani da makaman Faransa a Yemen din.
A makon jiya ne wata kafar yada labarai ta bankado cewa, ana amfani da makaman Faransa da suka hada da tankokin yaki da atilary kan mayakan Huthi a Yemen, al’amarin da ya sa aka yi wa gwamnatin Faransa ca.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi mahukuntan birnin Paris da hannu a laifukan yakin da aka aikata kan fararen hula a Yemen, in da kimanin mutane dubu 10 suka rasa rayukansu, baya ga miliyoyi da suka fada cikin barazanar yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu