Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Akwai sabani tsakanina da shugaban Faransa - Merkel

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Ludovic Marin/Pool/REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

A karon farko shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatar da cewa akwai sabanin ra’ayi tsakaninta da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Talla

Merkel ta bayyana haka ne yayin zantawa da jaridar Süddeutsche Zeitung ta kasar Jamus da aka wallafa a ranar Larabar da ta gabata.

A ‘yan watanin baya bayan nan dai shugabanin biyu sun fuskanci rashin fahimtar juna, kan batutuwa da dama, musamman dangane da soke cinikin saidawa Saudiya makamai da Jamus ta yi, biyo bayan kashe dan jarida Jamal Khashoggi, da ake zargin dan sarkin kasar Muhammad bin Salman da hannu a ciki, da kuma makomar nahiyar turai, sai kuma batun ficewar Britaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai na karin lokacin da aka yi mata

Sai dai shugabar gwamnatin ta Jamus ta bayyana a cewa an samu ci gaba mai yawa sakamakon huldar diflomasiyar da ke tsakanin kasarta ta Jamus da Faransa, musaman kan sha’anin da ya shafi tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.