Amurka

Trump yace Amurka na bukatar tarin baki kwararru kan sana'o'i

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump yace kasar na bukatar tarin baki wadanda suka kware akan sana’oi daban daban.

Talla

Trump ya bayyana haka ne yayin gabatar da sabon shirin gwamnatinsa dangane da karbar baki.

Shugaban yace sabon shirin zai bada damar kara yawan irin wadannan baki kwararru daga kashi 12 zuwa kashi 57 ko fiye da haka, domin ganin Amurka ta tsaya daidai da sauran kasashen duniya.

Trump ya kara da cewa Amurka na alfahari da bude kofar da za ta yi, amma dole wadanda za su amfana da wannan shirin ya kasance kwararru ne wadanda kuma suka iya Turancin Ingilishi da za su zana jarabawa kafin samun damar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.