Turai

Masu ra'ayin rikau sun yi rinjaye a zaben 'yan majalisun Turai

Marine Le Pen, Shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau a Faransa.
Marine Le Pen, Shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau a Faransa. Bertrand GUAY / AFP

Sakamakon farko na zaben shiga majalisar dokokin Turai mai kujeru 751 da aka gudanar cikin kasashe 21 jiya lahadi, na nuni da cewa akalla 51% na jama’a ne suka fito don kada kuri’unsu.

Talla

Sakamakon zaben ya bai wa masu zazzafen ra’ayi daga Faransa, Birtaniya da kuma Italiya damar samun karin wakilci a cikin zauren majalisar.

Alkalumman da aka ta tattara a Faransa sun tabbatar da cewa jam’iyyar da ke karkashin jagorancin Marine Le Pen ce ke sahun gaba da sama da kashi 24% na kuri’un, fiye da jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron da ta samu kasa da kashi 23%.

A kasar Poland, jam’iyyar masu ra’ayin rikau da ke karagar mulki ce ta lashe zaben da sama da kashi 42%, yayin da ba tare da wata tantama ba, jam’iyyar ‘yan gurguzu da ke mulkin Spain za ta fi gaba da kasancewa babbar wakilya a sabuwar majalisar.

A Romania masu goyon bayan ci gaba da kasancewa a kungiyar Turai ne suka samu gagarumar nasara, sabanin kasar Hungry inda jam’iyyar da ke adawa da manufofin Turai ta Viktor Orban ta lashe zaben.

A can kuwa Italiya, jam’iyyar Firaminiista Matteo Salvini ce ke sahun gaba, kamar dai Birtaniya inda Nigel Farage mai fatan gaggauta ficewa daga Turai ta kara samun kujeru a zaben, yayin da a Jamus kasa mafi tattalin arziki a Turai, fira minista Angela Merkel ta fuskanci mummunan koma baya a zaben na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.