Birtaniya

Boris Johnson zai gurfana gaban kotu saboda karya kan Brexit

Tsohon Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson.
Tsohon Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson. REUTERS/Andrew Yates

Tsohon Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson, zai gurfana a gaban kotu, bisa zargin shirga karya a lokacin yakin neman zaben jin ra’ayin al’umma kan batun ficewar kasar daga kungiyar Turai.

Talla

Alkali kotun da ke birnin London Margot Coleman, shi ne ya sanar da daukar wannan mataki bisa bukatar wani attajirin kasar mai suna Marcus Ball, inda alkalin ya rubuta wa Johnson jerin zarge-zargen da ake yi masa domin ya shirya kare kansa.

A shekara ta 2016 lokacin yakin neman zaben ficewar Birtaniya daga cikin EU, Borris Johnson ya ce kasar na zubawa kungiyar kasashen ta Turai fan milyan 350, kimanin dala milyan 440 a kowane mako, kuma ba abin da kasar ke amfana da shi illa hasara.

Bayan gudanar da bincike a game da wannan zargi, alkalin kotun ya ce ya zama wajibi a aike wa tsohon sakataren harkokin wajen sammaci, saboda ya gurfana a gaban kotu domin amsa tambayoyi, tare da neman ya gabatar da hujja dangane da wancan ikirari.

Johnson, wanda tsohon magajin garin birnin London ne, manazarta na ganin cewa wannan zance ko shakka babu, zai iya shafar burinsa na tsayawa takara domin maye gurbin Fira Minista Theresa May wadda ke shirin sauka daga mukaminta a nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI