Trump ya bukaci Birtaniya ta fice daga EU ba tare da yarjejeniya ba
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake tsoma baki kan shirin ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai EU.
A Yau lahadi Trump ya shawarci duk wanda zai maye gurbin Fira Ministar Birtaniya mai barin gado Theresa May, ya jagoranci ficewar kasar daga cikin EU ba tare da cimma wata yarjejeniya da ita ba.
Yayin zantawa da jaridar Sunday Times, gabannin ziyarar da yake shirin kaiwa Birtaniya a ranar Litinin, Trump ya ce bai kamata sabon Fira Ministan kasar ya ji tsoron ficewa daga cikin EU ba tare da yarjejeniya ba, zalika ya mai bada shawarar kada Birtaniyar ta amince da biyan kudin rabuwar da kungiyar kasashen Turan ta yanka mata, da ya kai kimanin Euro biliyan 39.
A ranar 24 ga watan Mayu Theresa May ta sanar da murabus dinta yau Juma’a, inda ta ce za ta ajje aiki ranar 7 ga watan Yuni, a wani mataki da ta kira da abin takaici ganin yadda ta gaza tabbatar da bukatar kasar kan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu