Amurka

Manya 'yan kasuwan Amurka 200 sun goyi bayan zubar da ciki

Tutar Amurka
Tutar Amurka

Akalla manyan ‘yan kasuwa 200 suka amince da da wata budaddiyar wasika kan damar zubar da ciki, suna mai cewa kokarin da masu tsatsauraran ra’ayi ke yi na dakile wannan dama ba zai haifar wa ma’aikata da abokan hulda da mai ido ba.

Talla

Sun ce hakan na barazana ga damar samun lafiyar iyali da ma bunkasar tattalin arziki.

Fitattun shugabannin kamfanonin sadarwa da na yada labarai na cikin wadanda suka amince tare da sa hanun a wannan wasika, cikinsu har da shugaban Twitter Jack Dorsey da Stewart Butterfield na Slack.

Shugaban rukunin kamfanin yada labarai na Bloomberg Peter Grauer da na kamfanin kade kade na Atlantic Records Julie Greenwald na cikin wadanda suka amince da wannan wasika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.