Turai

Kasashen Turai za su hada hannu don lalubo batattun 'yan cirani

Wasu 'yan cirani bayan isowarsu gabar Tekun Meditereniya
Wasu 'yan cirani bayan isowarsu gabar Tekun Meditereniya © REUTERS/Tony Gentile/File Photo

Kasashen da ke gab da tekun Meditereniya sun sha alwashin hada hannu don fara wani aikin laluben ‘yan ciranin da suka bace a kokarinsu na tsallaka nahiyar Turai daga kasashen su.

Talla

Yayin wani taron hukumar kula da mutanen da suka bace ta duniya da ya gudana a birnin Hague na Holland, kasashen wadanda suka kunshi Cyprus, Girka da kuma Malta sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fara aikin laluben mutanen galibi ‘yan Syria da yaki ya raba da muhallansu.

Hukumar ta ICMP ta bayyana cewa akwai akalla mutane dubu 18 da dari 5 da suka bace a hanyarsu ta tsallakawa Nahiyar Turai tun daga shekarar 2014 kawo yanzu, matakin da ta ce akwai bukatar hada hannu tsakan-kanin kasashen gab da tekun don lalubensu.

Sai dai yayin Taron kasar Italiya wadda ke matsayin madakata ta farko ga galibin ‘yan ciranin da ke tsallakawa Turai, ta ki amincewa da sanya hannu ko tallafawa wajen gudanar da aikin laluben ‘yan ciranin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.