Isa ga babban shafi
Faransa

Tsananin zafi ya tilasta rufe makarantu dubu 4 a Faransa

Yadda wasu mutane ke neman yanayin sanyi cikin ruwa a birnin Paris, sakamakon tsanantar yanayin zafi a sassan kasar Faransa.  25/6/2019.
Yadda wasu mutane ke neman yanayin sanyi cikin ruwa a birnin Paris, sakamakon tsanantar yanayin zafi a sassan kasar Faransa. 25/6/2019. ©REUTERS/Charles Platiau
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Faransa ta fuskanci yanayi mafi zafi cikin shekaru sama da 10 a karshen makon nan, bayanda matakin zafin a ma’aunin Celsius ya kai digiri 44.3 a sassan kasar.

Talla

Tuni dai aka samu rahotannin hasarar rayuka a sassan nahiyar Turai, a dalilin yanayin zafin da ke daga tsananta.

Faransa, Spain, Italiya da kuma wasu yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Turan iftila’in tsananin zafin yafi shafa.

Akalla makarantu dubu 4000 aka rufe a sassan Faransa don kaucewa zafin, gudun sake fuskantar rasa rayukan da aka yi a kasar cikin shekarar 2003, inda akalla mutane dubu 15 suka halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.