EU-BRUSSELS

Taro shugabannin EU ya tashi baram-baram a Brussels

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. ©REUTERS/Yves Herman

Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai, sun bata tsawon daren wayewar garin yau Litinin su na tafka mahawara kan yadda rabon manyan mukamai zai gudana a jagorancin kungiyar bayan zabe, ko da dai har zuwa kammala taron sun gaza cimma matsaya, bayan da bangaren adawa ya yi tirjiya kan tsarin.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwararsa ta Jamus Angela Merkel ce suka samar da shawarar gudanar da taron, yayin kebantacciyar ganawar da ta gudana tsakaninsu a taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da ya gudana a birnin Osaka na Japan.

Sai dai da alama, kwallaiya ba ta biya kudin sabulu ba, game da dubarar ta Merkel da Macron, la’akari da yadda bangaren adawa galibi masu ra’ayin rikau suka yi watsi da tsarin rabon mukaman, wanda aka shafe tsawon makwanni ana muhawara kan sa tun bayan kammala zaben Nahiyar cikin watan shekaran jiya.

Karkashin tanadin yarjejeniyar Sushi dai shugabannin kasashen kungiyar 28 ne za su hadu wajen zaben Frans Timmermans a matsayin shugaban hukumar kungiyar ta EU maimakon takwaransa na Jamus Manfred Weber na Conservative.

Haka zalika yarjejeniyar ta yi tanadin bai wa Weber damar tsayawa don zabarsa a matsayin kakakin majalisar kungiyar ta EU yayinda dan takarar jam’iyyar liberal kuma ke da damar zama shugaban majalisar shugabannin kasashen na Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI