Faransa

Zakara ya gurfana gaban kotu bisa zargin takurawa makwabta

Wani Zakara a harabar kotun garin Rochefort dake yammacin Faransa, yayin sauraron shari'ar zargin takwaransa da takurawa makwabta.
Wani Zakara a harabar kotun garin Rochefort dake yammacin Faransa, yayin sauraron shari'ar zargin takwaransa da takurawa makwabta. AFP/XAVIER LEOTY

A wani labari mai kama da almara, wasu dattijai guda biyu a Faransa sun gurfanar da wani zakaran makocinsu a garin Rochefort, saboda zargin da suke masa cewar carar da yake yi da asuba na tashinsu daga bacci.

Talla

Zakaran mai suna Maurice bai samu halartar zaman kotun ba, kamar yadda suma masu kararsa suka kauracewa zaman kotun, amma masu goyan bayan zakaran sun kwaso nasu zakarun inda suka cika mamaye kotun.

Wannan shari’a ta dauke hankalin jama’a, bai wai dan hoton zakaran na tambarin kasar Faransa ba, sai dai ana ganin karar wani cin zarafi ne ga mazauna kauye wadanda rayuwarsu ta kunshi zama da irin wadannan tsuntsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI