Majalisar Dinkin Duniya

Bakin - haure da 'yan gudun hijira na cikin mummunan yanayi a Amurka - MDD

António Guterres, Secretário-Geral da ONU. 13 de Dezembro de 2018.
António Guterres, Secretário-Geral da ONU. 13 de Dezembro de 2018. Jonathan NACKSTRAND / AFP

Shugabar Hukumar kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michele Bachelete ta ce ta kadu da ganin irin yanayin da bakin haure da ‘yan gudun hijira ke ciki a cibiyoyin da ake tsare da su a Amurka, biyo bayan rahoton dake cewa akwai cinkoso da kwayoyin cuta a dakunan.

Talla

A wata sanarwa, Bachelete ta ce, a matsayinta ta likitar yara, uwa, kuma tsohuwar shugabar kasa, ta kadu matuka da ganin yadda ake tilasta wa yara kwanciya a kasa, a inda a ke da cinkoso, ga karancin abinci da rashin tsaftataccen muhalli kuma babu kulawa ta bangaren lafiya.

Ko a makon da ya gabata, sai da wani rahoto daga ma’aikatar tsaron cikin gida na Amurka ya yi kashedi kan cinkoso mai hadari na mutane a cibiyoyin da ake tsare da dubban bakin - haure da ‘yan cirani da suka tirje kan sai sun zauna a Amurka, akasarinsu wadanda suka tsere wa rikici da talauci a Tsakiyar nahiyar Amurka.

Wasu jaridun Amurka biyu sun wallafa wani labarin dake kwatanta ofishin sintirin kan iyaka da ke garin Clint a jihar Texas, a matsayin wuri mai cike da daruruwan yara masu sanye da tufafi mai dauda da aka cushe a dakin tsare masu laifi mai cike da kwayoyin cuta.

Shugaba Donald Trump ya ce labarinsu na kanzon kurege ne, yana mai cewa zai jagoranci rangadin wurin da manema labarai.

Bachelete ta yi kira da a tausaya, tana mai jaddada cewa wadanda suka tsinci kansu a wadannan cibiyoyi sun yi doguwar tafiya tare da ‘yayansu, da zummar neman kariya da tsare mutuncinsu, a yunkurinsu na tsere wa rikici da yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.