Birtaniya-Tarayyar Turai

Kamata ya yi Birtaniya ta janye batun ficewa daga EU- Ursula

'Yar takarar Ursula von der Leyen
'Yar takarar Ursula von der Leyen REUTERS / Francois Lenoir

‘Yar takarar shugabancin Majalisar kungiyar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen, ta bayyana fatan Birtaniya ta yi watsi da batun ficewa daga cikin kungiyar, ta na mai kashedin cewa dole Birtaniyar ta dau alhakin duk wata matsalar da za ta biyo baya sakamakon ficewar.

Talla

Von der Leyen ta ce, yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da Firaminista Theresa May amma ‘yan majalisar dokokin kasar suka yi fatali da shi mai kyau ce, tana mai tsegunta cewa idan ta samu damar jagorancin kungiyar, ba za ta yarda da wata yarjejeniyar da ta wuce waccan ba.

Ta kafe cewa babu wani sauyi da za samu game da matsayin kungiyar kan yankin Ireland, sannan ta yi wa mutane biyun da ke dakon darewa kan mukamin Firaminista kashedin cewa, makomar dangantaka tsakanin Birtaniya da kungiyar Tarayyar Turai za ta ta’allaka ne da yadda aka rabu.

Mutane biyun dai da ke neman mukamin Firaminista a Birtaniya, Boris Johnson da Jeremy Hunt sun sha alwashin sake komawa teburin tattaunawa don samun yarjejeniyar da ta dara wacce Firaminista mai barin gado, May ta samu.

Shekaru 3 bayan kuri’ar raba gardama mai cike da al’ajibi da aka kada don barin kungiyar kasashen Turai, batun ya ci gaba da raba kawunan ‘yan Birtaniya, kuma Van der leyen ta ce tana fatan Birtaniya ba za ta fice ba, amma dole kasar ta warware kiki – kaka da batun ficewar ya janyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI