Faransa

Majalisar Faransa ta amince da karin haraji kan manyan kafofin sadarwa

Majalisar Dokokin Faransa ta amince da dokar sanyawa manyan kafofin sadarwar duniya irinsu Amazon, Google, Apple da Facebook harajin kashi uku cikin ribar da suke samu duk shekara 11 ga watan Yuni 2019.
Majalisar Dokokin Faransa ta amince da dokar sanyawa manyan kafofin sadarwar duniya irinsu Amazon, Google, Apple da Facebook harajin kashi uku cikin ribar da suke samu duk shekara 11 ga watan Yuni 2019. Reuters

Faransa ta zama kasa ta farko daga manyan kasashen da Majalisar Dokokinta ta amince da dokar sanyawa manyan kafofin sadarwar duniya harajin kashi 3 na ribar da suke samu a shekara duk da adawar da shugaba Donald Trump keyi da shirin.

Talla

Ita dai wannan sabuwar dokar ana saran ta cike gibin da ake samu wajen harajin da wadannan manyan kamfanonin sadarwa ke biya a shekara irin su Google da Apple da Facebook da kuma Amazon.

Dokar bata fuskanci matsala ba daga Yan Majalisun Dattawa wajen amincewa da ita, ganin cewa tuni Majalisar wakilai ta amince da kudirin.

Tuni shirin amincewa da dokar ya haifar da martani mai zafi da kuma barazana daga shugaba Donald Trump na Amurka wanda ya baiwa jami’an sa umurnin gudanar da bincike akai da kuma barazanar daukar matakin ramuwa kan Faransa kamar yadda yake yiwa China wajen dora mata haraji.

Babban jami’in kasuwancin Amurka, Robert Lighthiser ya bayyana cewar Amurka ta damu da wannan doka wanda zai yiwa kamfanonin ta illa, yayin da ministan tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire yace babu wata barazana daga Amurka da za tayi tasiri a kasar, domin Faransa kasa ce mai cin gashin kan ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI