Faransa

Bikin murnar kwallon kafa ya juye zuwa tarzoma da kwasar ganima

Shagon saida baburan Ducati a Champs-Elysees da ke tsakiyar birnin Paris da masu tarzoma suka sace kayayyaki da dama.
Shagon saida baburan Ducati a Champs-Elysees da ke tsakiyar birnin Paris da masu tarzoma suka sace kayayyaki da dama. AFP

Shaguna masu yawa aka fasa gami da sace kayayyaki a birnin Paris, yayin gangamin murnar da daruruwan yan Algeria suka yi, bayan fitar da Ivory Coast daga gasar cin kofin nahiyar Afrika, sai dai daga bisani taron ya juye zuwa tashin hankali.

Talla

An dai samu tashin hankalin ne a tsakiyar birnin Paris da kuma yankin Vieuk Port da ke birnin Marsielle.

A yankin Champs Elysees da ke danganewa da fadar gwamnatin Faransa, daruruwan magoya bayan kwallon kafar Algeria sun fasa manyan shagunan kayayyaki biyu, ciki har da na babur din Ducati, inda suka sace tulin hulunan kwano, safar hannu, har da baburan na Ducati.

Juyewar gangamin murnar zuwa tashin hankali da barnata dukiya ne yasa jami’an tsaro amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa magoya bayan kwallon kafar a birnin na Paris da kuma Marsielle.

A kudancin birnin Montpellier kuwa, wani magoyi bayan kwallon Algeria ya halaka wata mata tareda jikkata jaririnta, sakamakon kwacewar da motarsa ta yi, yayin wasan nuna murnar doke Ivory Coastda suka yi.

A halin yanzu Yan Sandan Faransa suna tsare da mutane 73, ciki har da kananan yara 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI