Amurka

Jami'an tsaron Amurka za su soma kamen bakin-haure

Akalla bakin-haure 2000 ake sa ran maidawa kasashensu daga Amurka.
Akalla bakin-haure 2000 ake sa ran maidawa kasashensu daga Amurka. Reuters

Jami’an tsaron Amurka sun soma shirin farautar bakin-haure da yan gudun hijirar da ke zaune a kasar ba tare da izini ba.

Talla

Ana sa ran hadin gwiwar jami’an shige da fice da na Kwastam su kai samame a yankunan manyan biranen Amurka akalla 10, domin kame bakin-haure dubu 2000 da suka shiga kasar a baya bayan nan.

Kafin wannan lahadi, daruruwan mutane karkashin jagorancin kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zangar neman dakatar da samamen kame bakin-hauren, ammma shugaban Amurka Donald Trump yayi watsi da bukatar.

A baya shugaba Trump ya sha alwashin maida jimillar bakin-haure miliyan guda da ke zaune a Amurka kasashensu, amma daga bisani ya janye matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI