Faransa

Yan sandan Faransa sun kame karin 'yan Algeria 282 saboda tarzoma

Wasu daga cikin 'yan Algeria, yayin murnar kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika.
Wasu daga cikin 'yan Algeria, yayin murnar kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika. AFP

Ma’aikatar cikin gidan Faransa tace bayyana kame yan kasar Algeria 282, sakamakon yadda bikin murnar da suka yi a ranar lahadi, kan samun nasarar kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin Afrika ta rikide zuwa tarzoma da barnata kayayyaki.

Talla

Ma’aikatar cikin gidan tace an kame yan Algeria da suka tayar da hankula ne a sassan kasar ta Faransa, yayin bikin murnar yadda suka doke Najeriya da 2-1 a wasan kusa da na karshe.

A makon jiya ma sai da jami’an tsaron na Faransa suka kame yan Algeria 73, mafi akasarinsu a birnin Paris, sakamakon yadda bikin murnar doke Ivory Coast a zagayen kwata final na gasar cin kofin ta nahiyar Afrika.

Yayin bikin murnar a waccan lokacin dai, wasu ‘yan kasar ta Algeria sun yi amfani da damar wajen fasa manyan shagunan kayayyaki biyu, ciki har da na babur din Ducati, inda suka sace tulin hulunan kwano, safar hannu, har da babura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI