Amurka

Trump ya sake muzanta 'yan majalisun Amurka mata

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada matsayinsa kan ‘yan majalisun kasar mata guda 4 dake cigaba da sukar manufofinsa, inda yace idan basu gamsu da rayuwa a Amurka ba, su fice su koma kasar su.

Talla

Yayin jawabi a fadar shugaban kasa, Trump ya bayyana ‘yan majalisun a matsayin gwanayen korafi, wadanda basa son Amurka, sun kuma tsani kasar.

Donald Trump kan muzanta 'yan majalisun Amurka mata

Sai dai duk da kalaman na Trump, ‘yan majalisun wakilai 4 da shugaba Donald Trump ya bukaci su koma kasarsu ta asali sun bayyana cewar babu wanda ya isa ya hana su fadin albarkacin bakinsu, bayan da shugaban ya ci gaba da sukar manufofinsu.

Alexandria Ocasio-Cortez da Ayyana Pressley da Rashida Tlaib da kuma Ilhan Omar sun kare sukar shugaban da suke inda suka nesanta manufarsu da zargin da yake musu na nuna wariyar jinsi.

Yan majalisun da suka bayyana matakin shugaban a matsayin yunkurin kawar da kai kan abinda yake faruwa, sun ce zasu ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI