Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta yi watsi da neman diyyar hadarin jirgin ruwan 1994

Masu zaman sauraron shari'ar ta yau a Kotu kan hadarin na shekarar 1994
Masu zaman sauraron shari'ar ta yau a Kotu kan hadarin na shekarar 1994 France 24
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 Minti

Kotun Faransa da ke zamanta a wajen birnin Paris ta ki amincewa da bukatar tilastawa kamfanin jirgin ruwan Estonia biyan diyyar mutanen da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwan na shekarar 1994.

Talla

Yayain zaman kotun na yau da wasu da suka tsira da rayukansu a hadarin suka shigar da kara sun bukaci tilastawa kamfanin biyan diyyar mutanen da suka rasa rayukansu a hadarin wanda shi ne mafi muni da nahiyar Turai ta fuskanta tun bayan hadarin jirgin Titinic.

Yayin hadarin jirgin dai wanda ya faru a shekarar 1994, cikin babban tekun yankin Baltic, akalla mabanbantan fasinja daga kasashen duniya 17 su kimanin 852 daga cikin fasinja 989 da ke cikin jirgin ne suka rasa rayukansu, wanda a wancan lokaci aka alakanta da gurbacewar yanayi.

Sai dai bayan dogon bincike a shekarar 1997, sakamako ya nuna cewa hadarin ya faru ne sanadiyyar gazawar wata na'ura da ta kai ga kullewar injinan da ke sarrafa tafiyar jirgin a tsakiya teku.

Cikin shekarun baya-bayan nan ne fiye da fasinjoji 1000 da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin suka bukaci lallai kotu ta fara sauraren karar kan kamfanin jirgin na Estonia Ferry mallakin kasar Jamus da ya samu shaidar kwarewa daga Faransa.

A cikin watan Aprilun da ya gabata ne kotu ta amince da fara sauraren karar don neman diyyar akalla yuro miliyan 40 daga kamfanonin biyu.

Sai dai bayan zaman kotun na yau taki amincewa da bukatar inda ta ce har yanzu masu shigar da karar basu da cikakkiyar hujja.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.