Isa ga babban shafi

Wutar Daji na ci gaba da barna a Portugal

Kawo yanzu dai babu addin mutanen da suka rasa rayukansu a wutar dajin wadda ta faro tun a jiya Asabar.
Kawo yanzu dai babu addin mutanen da suka rasa rayukansu a wutar dajin wadda ta faro tun a jiya Asabar. REUTERS/Costas Baltas
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Fiye da masu aikin kashe gobara dubu guda ne, yanzu haka ke ci gaba da kai dauki don kashe wutar dajin da ta taso a tsakiyar kasar Portugal wadda ta haddasa kwashe kauyuka da dama baya ga hallaka tarin jama’a.

Talla

Wutar dajin wadda ita ce mafi muni da Portugal ta fuskanta tun bayan ta shekarar 2017 wadda ta hallaka tarin jama'a, yanzu haka ta watsu sassa 3 a dajin Castelo Branco mai tazarar kilomita 200 da birnin Lisbon .

Rahotanni sun bayyana cewa akwai jiragen Shalkwafta akalla 20 baya ga manyan jirage da ke kai dauki a kokarin kashe gobarar.

Tuni dai aka kwashe wadanda gobarar ta jikkata zuwa birnin Lisbon don basu kulawar gaggawa ciki kuwa har da jami’an kashe gobara guda 4.

Kawo yanzu dai babu alkaluman da ke nuna mutanen da suka mutu a wutar dajin.

Tun bayan farowar gobarar a jiya Asabar, kauyuka fiye da 10 da ke gab da dazukan aka kwashe don tseretar da rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.