Bakonmu a Yau

AbdulHakeem Garba Funtua kan zaben sabon Fira Ministan kasar Birtaniya

Sauti 03:43
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya.
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya. REUTERS/Toby Melville

Kamar yadda kuka ji a cikin labaran duniya, Jam’iyyar Conservative da ke Birtaniya, ta zabi Boris Johnson a matsayin sabon shugaba, wanda zai maye gurbin Theresa May a matsayin Firaminista.Boris Johnson ya samu kuri’u 92,153, yayin da abokin takarar sa Jeremy Hunt ya samu 46,565.Johnson ya sha alwashin kammala fitar da kasar daga kungiyar Turai ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.Dangane da kalubalen da ke gabansa, mun tattauna da Dr AbdulHakeem Garba Funtua kuma ga tsokacin da yayi akai.